logo

HAUSA

Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Na Farko Ya Fara Yin Bulaguro

2024-01-01 20:01:39 CMG Hausa

Da yammacin yau ne, babban jirgin ruwa na farko na kasar Sin mai suna Adora Magic City, ya tashi daga tashar jiragen ruwa dake birnin Shanghai, don yin bulaguron kasuwanci na farko, inda ya bude wani sabon babi a fannin kera jiragen ruwa da ma masana’antar tafiye-tafiye ta ruwa na kasar.

Jirgin da ke dauke da fasinjoji sama da dubu uku, ya taso ne daga tashar jiragen ruwan kasa da kasa ta Wusongkou dake Shanghai, kuma ana sa ran zai isa yankin arewa maso gabashin Asiya, da suka hada da kasashen Japan da Koriya ta Kudu, kafin ya dawo ranar Lahadi.

Jirgin ruwa na Adora Magic City, yana da tsayin mita 323.6, da nauyin tan 135,500, kuma yana iya daukar fasinjoji 5,246 a cikin dakunan baki 2,125, kamar yadda wadanda suka kera shi, wato kamfanin CSSC na Shanghai Waigaoqiao (SWS), suka bayyana.

Jirgin ruwan yana da hawa 16, da jimillar murabba'in fadin mita dubu arba’in na wurin zama da wurin da jama’a za su iya shakatawa

Babban manajan kamfanin SWS, Chen Gang ya bayyana cewa, yadda aka kera manyan jiragen ruwa na bulaguro kamar Adora Magic City, ya nuna karfin da kasar Sin ta ke da shi na iya kera jiragen ruwa.

A watan Nuwanban bara ne aka gabatar da jirgin, bayan shafe shekaru takwas ana gudanar da binciken kimiyya da shekaru biyar na tsarawa da kerawa.(Ibrahim)