logo

HAUSA

Xi Da Kim Sun Ayyana Shekarar 2024 A Matsayin Shekarar Abokantaka Tsakanin Sin Da Koriya Ta Arewa

2024-01-01 16:09:46 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim Jong Un, a yau Litinin sun ayyana shekarar 2024 a matsayin shekarar abokantaka tsakanin Sin da Koriya ta Arewa, tare da kaddamar da wasu ayyuka.

Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da Kim, babban sakataren jam’iyyar ma’aikata ta Koriya ta Arewa, kuma shugaban Koriya ta Arewa, sun bayyana hakan ne a yayin musayar sakon taya juna murnar sabuwar shekara.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Koriya ta Arewa wajen daukar cikar shekaru 75 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, da kuma shekarar abokantaka tsakanin Sin da Koriya ta Arewa, a matsayin wata dama ta ci gaba da dadaddiyar zumuncinsu, da zurfafa amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare, da kara yin mu'amala da hadin gwiwa, da tabbatar da cewa kasashen biyu za su ci gaba da yin hadin gwiwa da juna, da tabbatar da ganin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta ci gaba da samun bunkasuwa sosai, don amfanar jama'ar kasashen biyu, da ci gaba da ba da sabbin gudummawa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. (Yahaya)