logo

HAUSA

Shugaban Chadi: Kasarsa ta koma hanyar shiga sabuwar jamhuriya

2024-01-01 16:27:59 CMG Hausa

 

Shugaban rikon kwarya na kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno ya bayyana cewa, kasar ta kama hanyar shiga sabuwar jamhuriya bisa 'yanci da adalci da kuma martabar kasa, bayan amincewa da sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Deby ya ce, sabon kundin tsarin mulkin kasa da ya kafa jamhuriya ta biyar, zai kafa sabon tsarin shugabanci mai cike da daidaito, karfi da cibiyoyi na jamhuriya da "demokuradiya na gaskiya daga tushe" ta hanyar baiwa kananan hukumomi ‘yancin tafiyar da harkokinsu.

A ranar Alhamis ne kotun kolin kasar Chadi ta sanar da cewa, an amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar a zaben raba gardama da aka gudanar a ranar 17 ga watan Disamba, inda ya samu amincewa da kashi 85.90 cikin dari. (Ibrahim)