logo

HAUSA

Xi Da Biden Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 45 Da Kulla Huldar Diplomasiyya Tsakanin Kasashensu

2024-01-01 15:34:48 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden, sun yi musayar sakon taya juna murnar cika shekaru 45 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.

A cikin sakonsa, shugaba Xi ya ce, kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Amurka, wani babban lamari ne a tarihin alakar dake tsakanin kasashen biyu da ma na kasa da kasa.

Xi ya ce, a cikin shekaru 45 da suka gabata, alakar kasashen Sin da Amurka ta fuskanci wasu ‘yan matsaloli, amma baki daya ta ci gaba, wanda ba wai kawai ta kyautata jin dadin jama'ar kasashen biyu ba, har ma ta inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata a duk duniya.

Ya kara da cewa, tarihi ya riga ya tabbatar kuma zai ci gaba da tabbatar da cewa, mutunta juna, zaman lafiya da hadin gwiwa da samun moriyar juna, ita ce hanyar da ta dace kasashen Sin da Amurka su daidaita da juna, a matsayinsu na manyan kasashe biyu. Kuma ya kamata ta zama alkiblar kokarin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a sabon zamani.

Xi ya jaddada cewa, a shirye yake ya yi aiki tare da Biden, don ci gaba da tafiyar da dangantakar kasashen biyu, ta yadda hakan zai amfanar da kasashen biyu da jama'arsu, da kuma sa kaimi ga zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya.

A cikin tasa wasikar taya murna, shugaba Biden ya ce, tun lokacin da aka kulla huldar diplomasiyya a shekarar 1979, dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin, ta samar da wadata da damammaki a kasashen Amurka, Sin da ma duniya baki daya. Yana kuma fatan dorawa kan ci gaba da magabatansa suka samu, da dimbin tarurruka da tattaunawar da ya yi da shugaba Xi, don ci gaba da inganta dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin.(Ibrahim)