logo

HAUSA

An sake zabar Felix Tshisekedia matsayin shugaban DR Congo

2024-01-01 16:16:19 CMG Hausa

 

An sake zabar Felix Tshisekedi a matsayin shugaban kasar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo na wa’adin shekaru biyar, inda ya samu kashi 73.34 cikin dari na yawan kuri’un da aka kada a zaben da aka gudanar a ranar 20 ga watan Disamban shekarar bara, kamar yadda hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ta bayyana a ranar Lahadi.

Moise Katumbi, dan takara daga cikin ’yan adawa, shi ya zo na biyu da samun kusan kashi 18 cikin dari na kuri’un da aka kada, a cewar hukumar.

An shirya rantsar da zababben shugaban kasar a ranar 20 ga watan Janairun shekarar 2024, bayan kotun tsarin mulkin kasar ta amince da sakamakon zaben a ranar 10 ga watan Janairu. (Yahaya)