logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabin murnar sabuwar shekarar 2024

2023-12-31 21:22:11 CMG Hausa

A jajiberen sabuwar shekarar 2024 da ke tafe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabin murnar sabuwar shekara ta babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG da yanar gizo. Inda ya takaita hanyoyin da kasar Sin ta bi da nasarori da ci gaba da ta samu a shekarar 2023, tare da fatan kasar Sin za ta samu wadata da ci gaba, kana duniyarmu za ta samu kwanciyar hankali da zaman lafiya a shekara ta 2024.

Xi ya yi amfani da kalmar Cigaba wajen takaita hanyoyin da kasar Sin ta bi a shekarar 2023, inda ya bayyana cewa, yadda al’ummar Sinawa ke jin dadin zaman rayuwa, da fama da ayyuka ya nuna kokarinsu na neman zama mai dadi, da yadda kasar Sin ke cike da kuzari. A yayin da tattalin arzikin Sin ya farfado, ana kuma gudanar da aikin raya kasa mai inganci. Tsarin masana’antun kasar ya kara kyautatuwa, yayin da sabbin muhimman masana’antu na zamani marasa gurbata muhalli suka samu saurin ci gaba. Haka kuma kasar Sin ta yi shekaru 20 a jere tana yin girbin hatsi. Yanayin muhalli ya kyautata matuka a kasar, yayin da ake farfado da yankunan karkara. Bugu da kari, an fara amfani da babban jirgin saman fasinja samfurin C919 a kasuwar jigilar fasinjoji. Babban jirgin ruwan fasinjoji da kasar Sin ta kera da kanta, ya gudanar da zirga-zirgar gwaji cikin nasara. An samu nasarar sauya ayyukan kumbunan Shenzhou a sararin samaniya, baya ga yadda jirgin da ke tafiya a karkashin ruwa kirar Fendouzhe ya samu nasarar zuwa teku mai matukar zurfi. Bisa ruhin Sinawa na dogaro da karfin kansu da dagewa wajen yin wani abu, kasar Sin ta samu manyan sabbin kirkire-kirkire.

Xi ya kuma yi amfani da kalmomin Hadin Kai Da Kasashen Duniya wajen bayyana yadda kasar Sin ta sauke nauyin da ke bisa wuyanta. Inda ya ce, Sin ta samu nasarar gudanar da taron kolin Sin da kasashen yankin Tsakiyar Asiya, taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa kan shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya. Baki daga sassa daban daban na duniya sun halarci tarurruka a jere da aka gudanar a kasar Sin.

Xi ya kuma nuna cewa, badi, za a cika shekaru 75 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin. Kasarsa za ta tsaya tsayin daka kan zamanantarwa mai salon kasar Sin. Kana ya ce, Sin na da babban burin da take fatan cimmawa, burin da ke shafar kowa, wato za a yi kokarin ganin al’ummar Sinawa na kara jin dadin zaman rayuwarsu, ta yadda kowa zai ji dadi da farin ciki, samun nasara da cimma burinsa.(Kande Gao)