logo

HAUSA

An cimma manyan nasarori a diflomasiyyar shugabancin Sin a 2023

2023-12-30 17:36:45 CMG

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce a shekarar nan ta 2023, Sin ta bunkasa alakar ta da manyan kasashen duniya, ta kyautata goyon baya da hadin kai tare da kasashe makwaftanta, da ma sauran kasashe masu tasowa.

Kaza lika, Sin ta bayar da gudummawar kwarewa, dangane da batutuwan dake haifar da sa-in-sa, a daya bangaren ta karfafa tushen hadin gwiwar abota tsakanin sassa daban daban.

Mao Ning, wadda ta bayyana hakan a jiya Juma’a, yayin taron manema labarai da ya gudana, ta ce karkashin managarcin tsarin diflomasiyyar shugabancin kasar, Sin ta shata sabuwar tafiya tare da bude sabbin babuka a fannin diplomasiyyarta a shekarar ta 2023. (Saminu Alhassan)