Taron harkokin waje da kasar Sin ta yi ya kafa alkibla ga makomar harkokin wajenta
2023-12-30 16:46:12 CMG Hausa
A karshen shekarar dake karewa wato 2023, kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ta gudanar da wani muhimmin taro kan harkokin diflomasiyyar kasar a Beijing, taron da ya gudana bayan shekaru biyar da rabi da suka gabata.
A shekaru goman da suka wuce, kasar Sin ta gudanar da harkokin diflomasiyyarta, daidai bisa taken “Wace irin duniya za’a gina, kuma ta yaya za’a gina”. Masharhanta na ganin cewa, wasu kasashen yammacin duniya na rika rura wutar rikici, da zummar nuna fin karfinsu a duniya, amma akasin haka, kasar Sin tana dada kokarin bayar da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a duniya.
A halin yanzu, babban hadarin da tsaron siyasar duniya ke fuskanta shi ne, matsawa sauran kasashe lamba, da rura wutar fito-na-fito tsakanin bangarori daban-daban, gami da yunkurin tada “sabon yakin cacar-baka” da wasu kasashen yammacin duniya ke yi, bisa damuwar gushewar karfinsu. Kana suna kuma yunkurin tallata ra’ayin nuna bangaranci da na bada kariya, bisa hujjar da suke kira “kawar da hadari”, da kawo cikas ga dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya. Sakamakon rashin kyawun ka’idojin daidaita harkokin duniya, ci gaban kasashe masu tasowa na fuskantar babban tsaiko.
Saboda haka, taron harkokin wajen da kasar Sin ta gudanar a wannan karo, ya bullo da wasu shawarwari guda biyu, wato raya duniya mai tsarin cudanyar bangarori daban-daban bisa adalci, da dunkule tattalin arzikin duniya baki daya, wanda ke kawo moriya ga kowa, abun da ya shaida zaman adalci da daidaito, da wakiltar bukatu, gami da muryoyin bai daya na kasashe daban-daban, da kuma samar da mafita ta kasar Sin ga shawo kan manyan matsaloli, da kalubalolin da duniya take fuskanta. (Murtala Zhang)