logo

HAUSA

Shugabannin Sin sun kalli wasan gargajiya na opera domin maraba da sabuwar shekarar 2024

2023-12-30 17:25:22 CMG

Shugabannin kasar Sin sun kalli wasan kwaikwayo na gargajiya na opera, domin maraba da sabuwar shekarar 2024.

Bikin wanda ya gudana a babbar cibiyar nuna fasahohi ta kasa dake birnin Beijing da yammacin jiya Juma’a, ya hallara jagororin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin(JKS) da na kasa, da suka hada da shugaba Xi Jinping, Li Qiang, Zhao Leji, Wang Huning, Cai Qi, Ding Xuexiang, Li Xi da Han Zheng, tare da sauran al’ummar kasar daga sassa daban daban.

Kafin fara nuna wasanni, shugaba Xi da sauran jagorori sun gabatar da gaisuwa ta musamman ga masu nuna wasannin. (Saminu Alhassan)