logo

HAUSA

Sin ta shafe shekaru 60 tana aikewa da ma’aikatan agajin jinya zuwa kasashen waje

2023-12-30 21:15:07 CMG Hausa

A farkon shekarun 1960, ba da jimawa ba da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin, wadda ke bukatar ci gaba, kuma ba ta da arziki sosai. Amma a lokacin, kasar Aljeriya da ta samu ‘yanci bada dadewa ba, ta yi kira ga sassan kasa da kasa ta kungiyar bada agaji ta Red Cross ta duniya, da su samar mata da tallafin jinya na gaggawa. Sin ce kasa ta farko da ta fito fili ta sanar da tura kwararrun likitocinta zuwa Aljeriya. Watakila kasashen duniya ba su taba tsammanin cewa, kasar Sin za ta shafe tsawon shekaru 60 tana gudanar da wannan aiki ba.

Nasarorin da kasar Sin ta samu cikin shekaru 60 a fannin samar da agajin jinya ga kasashen waje, sun baiwa dukkanin duniya zarafin fahimtar nauyin dake wuyan kasar. Sin kasa ce daya kadai a duk fadin duniya, da ke tsayawa wajen aikewa da tawagogin ma’aikatan agajin jinya zuwa kasashe masu tasowa cikin dogon lokaci.

Kawo yanzu, kasar Sin ta riga ta tura ma’aikatan samar da agajin jinya sama da dubu 30 zuwa kasashe da yankuna 76, da bada tallafin gina cibiyoyin likitanci da kiwon lafiya sama da 130, kuma adadin marasa lafiyar da likitocin kasar Sin suka kula da su ya tasam ma miliyan 300.

Bugu da kari, ma’aikatan samar da agajin jinya na kasar Sin suna himmatuwa wajen fadada ayyukan da suke yi a kasashen waje, musamman a wadannan shekaru 10, tun bayan da kasar ta bullo da ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a fannin kiwon lafiya, ayyukan likitocin kasar Sin sun fadada daga ceton rayuka da kulawa da marasa lafiya, har zuwa taimakawa kasashe wajen inganta tsarin kiwon lafiya, da karfafa kwarewarsu wajen samar da hidimomin kiwon lafiya. Wato daga samar da agaji, har zuwa inganta hadin-gwiwa mai dorewa, kasar Sin tana kokarin marawa kasashe daban-daban baya, don samun babban ci gaba.

Kasar Sin na kokarin zamanantar da kanta a halin yanzu, kuma a matsayinta na kasa mai tasowa mafi girma a duniya, a yayin da take raya kanta, tana kuma tsayawa ga taimakawa zamanantar da sauran kasashe.

Tsawon shekaru 60 ba karshe ne ba, akasin haka, sabon mafari ne. (Murtala Zhang)