Rawar da kasar Sin ta taka a duniya
2023-12-29 14:59:13 CMG Hausa
Kasar Sin ta riga ta zama babbar kasar da ke "samar da kyakkyawan tasiri, da ba da jagoranci wajen kirkiro sabbin fasahohi wadda ke sauke nauyin dake bisa wuyanta a duniya". An tabbatar da wannan ra’ayi a wajen taron aikin diplomasiyya na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da ya gudana tsakanin ranar 27 zuwa 28 ga wata, a birnin Beijing na kasar Sin.
A wannan shekara, an samu barkewar wutar yaki tsakanin bangarorin Falasdinu da Isra’ila. Don neman kwantar da kurar da ta tashi, kasar Sin ta yi kokarin sulhuntawa tsakanin bangarori masu ruwa da tsaki.
Duk da wannan shekarar da muke ciki, tattalin arzikin duniya na tafiyar hawainiya. Ganin haka ya sa kasar Sin ke kokarin raya tattalin arzikinta, don neman taimakawa farfadowar tattalin arzikin duniya.
A wannan shekara ta 2023, an samu cikar shekaru 45 da fara manufar bude kofa da gyare-gyare a gida a kasar ta Sin. Bisa hasashen da kungiyoyin kasa da kasa suka yi, kasar Sin za ta samar da kashi 1 cikin kashi 3 na gudunmawar da ta haifar da karuwar tattalin arzikin duniya.
Duk a wannan shekara, an samu cikar shekaru 10 da gabatar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, kana tsarin BRICS da na SCO dukkansu sun habaka, yayin da kungiyar kasashen Afrika ta AU ta zama mambar kungiyar kasashe da yankuna 20 mafi karfin tattalin arziki (G20).
A karshen shekarar 2023, huldar dake tsakanin kasar Sin da ta Amurka ta daidaita, inda haduwar shugabannin kasashen 2 a San Francisco na kasar Amurka ta samar da karin tabbaci ga huldar kasa da kasa.
Ko da yake ana ta fuskantar matsaloli a wannan zamanin da muke ciki, amma a ganin kasar Sin, yanayin ci gaba na tarihin dan Adam, da hadewar gamayyar kasa da kasa, ba zai canza ba.
A shekarar 2023, kasar Sin ta sauke nauyin dake bisa wuyanta. Sa’an nan ana sa ran ganin kasar ta kulla hulda mafi kyau tare da sauran kasashe, da kokarin kafa al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya tare da su, a shekarar 2024 mai zuwa. (Bello Wang)