logo

HAUSA

Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin za ta fara zaman taron shekara-shekara a ranar 5 ga watan Maris

2023-12-29 21:26:47 CMG

Majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) karo na 14 za ta fara zaman shekara-shekara karo na biyu a birnin Beijing a ranar 5 ga watan Maris na shekarar 2024, a cewar shawarar da zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ya yanke a yau Juma’a. An yanke shawarar ne a karshen zaman zaunannen kwamitin NPC da aka gudanar daga ranar Litinin zuwa Juma’a.

Baya ga haka, an ba da shawarar fara zama karo na biyu na kwamitin majalisar ba da shawara kan kan harkokin siyasa ta kasar Sin karo na 14 (CPPCC) a ranar 4 ga watan Maris na 2024 a nan birnin Beijing. An bayar da shawarar ne a taron majalisar shugabanni na kwamitin CPPCC karo na 14 na baya-bayan nan. (Yahaya)