logo

HAUSA

Xi Jinping ya yi jawabi a taron sabuwar shekara ta 2024 na majalisar CPPCC

2023-12-29 22:15:36 CMG

Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Juma'a ya yi jawabi a wurin taron da majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar(CPPCC) ta shirya don yin maraba da shekarar 2024.

Xi ya jaddada cewa, ciyar da babban aikin gina kasar Sin mai karfi gaba, da farfado da ita daga dukkan bangarori, ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin shi ne babban aikin jam’iyyar da na kasar kan sabuwar tafiya a wannan sabon zamani.

Kaza lika, Xi ya yi kira da a karfafa hadin kan ‘yan kishin kasa daga bangarori daban daban, da samar da manyan nasarori ta hanyar yin aiki tukuru, da kuma rubuta sabon babi kan zamanantar da kasar Sin tare. (Yahaya)