logo

HAUSA

Kwamitin kolin JKS ya gabatar da abubuwan da kasar Sin za ta yi a fannin harkar diplomasiyya a shekarar 2024

2023-12-29 15:03:34 CMG Hausa

An gudanar da taron aikin diplomasiyya na kwamitin kolin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, tsakanin ranar 27 zuwa ta 28 ga watan Disamban shekarar 2023 a birnin Beijing, fadar mulkin kasar, inda shugaba Xi Jinping na kasar ya gabatar da jawabi.

Ciki jawabinsa, shugaban ya yi bitar fasahohin da kasar Sin ta samu ta fuskar hulda da sauran kasashe, gami da gabatar da shiri kan aikin diplomasiyya na kasar.

An tabbatar a wajen taron da cewa, wani bangare mai muhimmanci da tunanin shugaba Xi Jinping a fannin aikin diplomasiyya ya kunsa, shi ne yunkurin kafa al'ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya, wanda shi ma ya kasance babban burin kasar ta Sin.

Sai dai ta yaya ake iya yin amfani da wannan yunkuri na kasar Sin wajen daidaita matsaloli a duniya? A gun wannan taro, shugaba Xi ya gabatar da dabaru guda 2, wato yayata ra'ayin kasancewar bangarori masu fada a ji da yawa a duniya, da dunkulewar tattalin arzikin duniya wadda za ta amfani kowa.

Dukkan kasashe, manya ko kanana, masu sukuni ko wadanke ke kan hanyar tasowa, suna cikin al'ummar dan Adam mai makomar bai daya. Wannan ra'ayi da kasar Sin ke da shi ya nuna yadda kasar take kokarin sauke nauyin dake bisa wuyanta, na tabbatar da ci gaban daukacin bil Adama. (Bello Wang)