logo

HAUSA

Sin ta tallafawa wadanda suka rasa matsugunnansu a Sudan ta kudu

2023-12-29 11:33:32 CMG Hausa

Ministan ma’aikatar ayyukan jin kai da shawo kan bala’u na kasar Sudan ta kudu Albino Akol Atak, ya ce wasu manyan motoci 6 dauke da fallen rufin daki na roba 26,145, sun isa birnin Juba, fadar mulkin kasar, domin tallafawa aikin samarwa ‘yan gudun hijira da suka tserewa muhallansu matsugunai. Kaza lika akwai karin motocin dakon nau’o’in kayayyaki daban daban daga Sin, da suka fara isa birnin Juba tun daga Alhamis.

Mista Akol Atak, ya ce za a yi amfani da tallafin na Sin wajen tsugunar da al’ummun dake komawa gidajen su, da masu gudun hijira dake sansanonin yada zango, da ma masu samun mafakar dindindin.

Ya ce Sudan ta kudu na fatan karbar karin wasu kayayyakin tallafin na Sin domin amfanin mutanen da suka rasa matsugunansu, wadanda darajarsu ta kai dala miliyan 1.4, kuma ana sa ran isarsu kafin karshen watan Janairun 2024 dake tafe.

Akol ya bayyana matukar godiya ga gwamnatin kasar Sin, bisa tallafinta ga Sudan ta kudu, wanda hakan ke tabbatar da sahihin kawancen dake tsakanin Sin da Sudan ta kudu. (Saminu Alhassan)