logo

HAUSA

Majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta kammala zaman zaunannen kwamitinta

2023-12-29 21:22:18 CMG

A yau Juma’a ne zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) ya kammala zama karo na bakwai a nan birnin Beijing.

A yayin rufe taron, ‘yan majalisar sun kada kuri’ar amincewa da dokar kamfanoni da aka yi wa kwaskwarima, da dokar tabbatar da wadatar abinci, da gyara ta 12 (XII) ga dokar laifuffuka, da kuma yanke shawarar gyara dokar Sadaka.

Har ila yau, sun amince da nada Dong Jun a matsayin ministan tsaro, da cire Tang Dengjie daga mukamin ministan harkokin jama'a da nada Lu Zhiyuan kan mukamin, da kuma sauke Hu Heping daga mukamin ministan al'adu da yawon bude ido tare da nada Sun Yeli a mukamin.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rattaba hannu kan umarnin shugaban kasa guda biyar don sanar da dokokin da shawarwarin. (Yahaya)