logo

HAUSA

Xi Jinping ya gana da wakilan da suka halarci taron tunawa da cika shekaru 60 da kasar Sin ta fara tura ma’aikatan agajin jinya ga kasashen waje

2023-12-29 17:29:45 CMG Hausa

An yi babban taron tunawa da cika shekaru 60 tun bayan da kasar Sin ta fara aikewa da rukunonin masu samar da agajin jinya zuwa kasashen waje, gami da karrama su a yau Jumma’a 29 ga wata a Beijing, inda babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar, wanda kuma shi ne shugaban kasar Sin, kana shugaban kwamitin sojan kasar, Xi Jinping ya gana da wakilai mahalarta taron, da taya su babbar murna, da gaisuwa da fatan alheri ga ma’aikatan samar da agajin jinya da a yanzu haka suke gudanar da aiki, ko wadanda suka taba gudanar da aikin a kasashen waje.

Memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne mataimakin firaministan kasar, Liu Guozhong ya halarci ganawar tare da yin jawabi, inda ya ce, kwamitin kolin na maida hankali sosai kan ayyukan samar da agajin jinya a kasashen ketare, kuma shi shugaban kasa Xi Jinping ya yaba matuka da nasarorin da aka samu a wannan fanni. A cikin shekaru 60 da suka gabata, ma’aikatan bada agajin jinyar kasar Sin sun himmatu wajen samar da magani, gami da nuna kauna ga jama’ar kasashe daban-daban, al’amarin da ya sa suka samu babban yabo daga gwamnatoci da al’ummomin kasashen.

Liu ya ce a sabon zamanin da muke ciki, ya kamata a ci gaba da yayata nagartattun halayen ma’aikatan bada agajin jinyar kasar Sin, da kokarin bude sabon babi ga aikin samar da agajin jinya a kasashen waje, domin kara bada gudummawa ga gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya a fannin kiwon lafiya.

Taron ya kuma karrama wasu fitattun rukunonin ma’aikatan bada agajin jinyar kasar Sin 30, gami da wasu daidaikun mutane 60, wadanda suka yi fice wajen aiki. Wakilan wadanda suka samu lambobin yabon sun kuma gabatar da jawabai. (Murtala Zhang)