logo

HAUSA

Xi Jinping ya gana da jakadun kasar Sin dake kasashen waje wadanda suka dawo Beijing don halartar taro

2023-12-29 20:26:42 CMG Hausa

Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban kasar, kana shugaban kwamitin sojan kasar, Xi Jinping, ya gana da dukkan jakadun kasar Sin dake aiki a kasashen waje, wadanda suka dawo Beijing don halartar taron ayyukan jakadun kasar Sin dake kasashen waje na shekara ta 2023, a babban dakin taron jama’a dake Beijing, a yau Jumma’a 29 ga wata, tare kuma da gabatar da wani muhimmin jawabi.

Shugaba Xi ya yaba da manyan nasarorin da aka samu a fannin harkokin diflomasiyya na wannan zamanin da muke ciki, da bukatar jakadun kasar Sin dake kasashen waje, da su kara nazartar muhimman abubuwan dake cikin babban taron jam’iyyar kwaminis ta kasar karo na 20, da taron harkokin waje na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis din, da kara koyo gami da aiwatar da tunanin gurguzu mai salon musamman na kasar Sin a sabon zamani, musamman wanda ya shafi harkokin diflomasiyya. Da kara fahimtar yanayin kasa da kasa da ake ciki, da babban nauyin dake wuyar kasar, a yayin da take tafiyar da harkokin waje, da daga tutar gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, a wani kokari na bude sabon babi ga harkokin diflomasiyyar kasar Sin masu salon musamman.

A nasa bangaren, memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya halarci ganawar, gami da gabatar da jawabi a wajen taron, inda ya bukaci a bude sabon babi ga harkokin diflomasiyyar kasar Sin masu salon musamman a sabon zamaninmu, daidai bisa jagorancin ra’ayin shugaba Xi a fannin diflomasiyya. (Murtala Zhang)