logo

HAUSA

An samu ci gaba yayin tattaunawar manyan jami’an soji na Sin da Amurka

2023-12-29 11:31:46 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Wu Qian, ya ce an samu ci gaba yayin tattaunawar da manyan jami’an soji na Sin da Amurka suka yi ta kafar bidiyo.

Wu ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na jiya Alhamis, inda ya ce a ranar 21 ga watan nan na Disamba, Liu Zhenli, hafsan hafsoshi a hedkwatar hadin gwiwa na manyan hafsoshin soji ta kwamitin koli na aikin sojan kasar Sin, tare da shugaban hafsan hafsoshin sojojin kasar Amurka Charles Brown, sun zanta ta kafar bidiyo, kuma tattaunawar tasu ta haifar da manyan nasarori.

Jami’in ya ce jagororin sun yi musayar ra’ayi mai zurfi, game da yadda za a aiwatar da ra’ayoyin bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, yayin taron San Francisco da ya gabata, da ma sauran batutuwa dake jan hankalin kasashen 2.

Ya ce Sin na fatan bangaren Amurka zai ingiza ci gaban kyakkyawar alakar dake tsakanin ta da Sin a fannin ayyukan soji, bisa daidaito da mutunta juna.

Game da shirye-shiryen musaya kuwa, Wu ya ce sashen tsaron kasa na kasashen biyu, na ci gaba da tattaunawa, zai kuma bayyana ci gaban da aka samu yadda ya kamata.  (Saminu Alhassan)