logo

HAUSA

Kasar Sin ta samu nasarori a fannin raya masana'antu

2023-12-29 11:17:04 CMG Hausa

Wani rahoton da aka gabatar a jiya Alhamis, dangane da aikin raya bangaren masana'antu a kasar Sin, ya nuna cewa, ma'aunin karfin masana'antu na kasar a shekarar 2022 ya kai maki 124.64, wanda ya zama kan gaba cikin alkaluman manyan tattalin arzikin duniya. Hakan a cewar rahoton, ya nuna wani yanayi mai armashi da Sin take ciki, ta fuskar raya masana'antu.

An ce, tsakanin shekarar 2020 da ta 2022, karuwar ma'aunin karfin masana'antu na kasar Sin ta zarce kashi 4% a duk shekara, lamarin da ya shaida jajircewar kasar a wannan fanni.

Ban da haka, rahoton ya ce, don tabbatar da ci gaban bangaren masana'antu a kasar Sin cikin sauri, ya kamata a ci gaba da amfani da fifikon da kasar ke da shi, irinsu samun manyan kasuwanni da iya samar da dimbin nau'ikan kayayyaki daban daban, da daidaita wasu bangarorin da ba su inganta sosai ba tukuna, ta yadda za a samar da wasu kamfanonin da suka kware kan wasu sabbin fasahohi, da wadanda suka kasance kan gaba a duniya a wani fanni, da kafa ingantattun kamfanoni da samfuran ciniki, da gungun kamfanoni na masana'antu, wadanda ke janyo hankalin mutanen mabambantan kasashe. (Bello Wang)