logo

HAUSA

NPC Tana Adawa Da Munanan Tanade-tanade Dake Da Alaka Da Sin A Cikin Dokar Ba Da Iznin Tsaron Amurka

2023-12-28 09:38:02 CMG Hausa

Mai magana da yawun kwamitin kula da harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC Xu Dong, ya bayyana rashin gamsuwa da rashin amincewa da kakkausar murya, kan munanan tanade-tanade dake da alaka da kasar Sin, a cikin dokar kasafin kudi ta shekarar 2024 mai nasaba da ba da iznin tsaron kasa ta Amurka, wacce kwanan nan aka sanyawa hannu.

Kakakin ya ce, kudirin da ke da alaka da wannan doka, yana magana ne kan batun yankin Taiwan, da ba da shawarar yin takara bisa manyan tsare-tsare da kasar Sin, da daukar Sin a matsayin barazana, da kuma yayata rage barazana a muhimman fannonin hulda da kasar Sin.

Ya bayyana cewa, hakan tamkar yin katsalandan ne ga harkokin cikin gidan kasar Sin matuka, da neman yin illa ga 'yancin kai, da tsaro da ci gaban kasar Sin, kuma ya keta yarjejeniyar da shugabannin kasashen Sin da Amurka suka cimma a taron San Francisco.

Kakakin ya ce, batun yankin Taiwan, ainihin tushen moriyar kasar Sin ne, kana ginshikin tushen siyasa a alakar kasashen Sin da Amurka, kuma jan layi na farko da ba za a ketare ba a dangantakar kasashen biyu.

Ya kuma jaddada cewa, kasar Sin a ko yaushe tana bin hanyar samun ci gaba cikin lumana, kana tanade-tanaden Amurka sun yi watsi da gaskiya, suna kuma ba da shawarar mayar da wata kasa saniyar ware, da siyasantar da batutuwan da suka shafi tattalin arziki, da fasaha da al'adu bisa son rai, da kokarin dakile mu'amala da hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Amurka.

Xu ya ce, mutunta juna, zaman tare cikin lumana, da hadin gwiwar samun nasara tare, su ne alkiblar kokarin yin hadin gwiwa tsakanin Sin da Amurka.(Ibrahim)