logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi tir da sanya hannun Amurka kan dokar tsaron kasa

2023-12-28 21:02:12 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Wu Qian, ya bayyana a yau Alhamis cewa, rundunar sojin kasar Sin ta nuna matukar rashin gamsuwa da kuma adawa da amincewar da Amurka ta yi da sanya hannu kan dokar ba da izinin tsaron kasa na shekarar kasafin kudi na 2024, wanda ke kunshe da abubuwan da ba su dace ba da suka shafi kasar Sin.

Wu ya ce, wannan mataki da suka dauka ba tare da wata hujja ba akan abin da suke kira “barazanar sojin kasar Sin” katsalandan ne ga harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma yana yin illa sosai ga ‘yanci kai, da tsaro da ci gaban kasar Sin. (Yahaya)