logo

HAUSA

Sojojin ruwan kasar Sin sun shafe shekaru 15 suna aikin tabbatar da tsaro a mashigin tekun Aden da gabar tekun Somaliya

2023-12-28 12:48:25 CMG Hausa

Tun a watan Disamban shekarar 2008 ne, kasar Sin ta fara aikewa da jiragen ruwan soja domin gudanar da aikin ba da kariya ga jiragen ruwan kasuwanci a mashigin tekun Aden da gabar tekun Somaliya.

A cikin shekaru 15 da suka gabata, tawagogi 45 dake kunshe da jiragen ruwan soja 150 da jami’an sojan ruwa na PLA dubu 35 da kasar Sin ta tura a jere, sun shiga wannan aiki, inda suka yiwa sama da jiragen ruwan kasuwanci na Sin da na kasashen waje 7,200 rakiya, ciki har da jiragen ruwa 12 masu sauke nauyin da shirin samar da abinci na duniya wato WFP ya yi musu.

Yunkurin sojojin ruwan PLA ya samu karbuwa sosai, inda jiragen ruwan ’yan kasuwa da dama daga wasu kasashe, suka nemi rakiya da ma kariya daga sojojin ruwan kasar Sin.

A cikin watan Satumban bana, tawaga ta 45 dake yiwa jiragen ruwa rakiya, ta tashi daga kasar Sin, inda ta fara tattaki don ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya a mashigin tekun Aden da gabar ruwan Somaliya. (Ibrahim Yaya)