logo

HAUSA

Rahoto: An samu matukar raguwar hadurra a wuraren ayyuka a kasar Sin

2023-12-27 10:08:37 CMG HAUSA

 

Wani rahoto da aka gabatarwa zaunannen kwamitin majalissar wakilan jama’a ta kasar Sin ko NPC, ya nuna cewa a shekarun baya bayan nan, ma’aikata a kasar na samun karin kariya daga hadurra yayin da suke gudanar da ayyukansu, don haka a kan samu hadurra, da rasa rayuka ’yan kalilan a yanzu idan an kwatanta da na shekarun baya can.

An gabatarwa NPC wannan rahoto ne a jiya Talata, bayan da kwamitin ya umarci wata tawagar masu sanya ido da ta nazarci yadda ake aiwatar da dokar bayar da kariya daga hadurra ga ma’aikata.

Rahoton ya nuna cewa, ya zuwa shekarar 2018, hadurra da aka samu a wuraren ayyuka sun ragu da kaso 80.8 bisa dari, kana ya zuwa shekarar 2022 adadin ya ragu da kaso 51.4 bisa dari, idan an kwatanta da shekaru biyar-biyar kafin shekarun.

Har ila yau, matsakaicin adadin manyan hadurran da a kan samu a wuraren ayyuka a duk shekara ya ragu da kaso 37.6 bisa dari in an kwatanta da na shekaru 5 kafin 2018, da kuma kaso 16.2 bisa dari idan an kwatanta da na shekaru 5 kafin 2022. (Saminu Alhassan)