logo

HAUSA

Ci gaba da gudanar da sha’anin da Mao Zedong ya kaddamar, shi ne abu mafi dacewa game da tunawa da shi

2023-12-27 10:09:36 CMG HAUSA

 

Jiya Talata, kwamitin tsakiyar JKS ya yi taro a babban dakin taron jama’a da ke birnin Beijing, fadar mulkin kasar, don tunawa da cika shekaru 130 da haihuwar marigayi Mao Zedong, wanda ya taka rawar gani wajen kafa jamhuriyar jama’ar kasar Sin.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana shi a matsayin mutum na farko da ya hada tunanin Markisanci da halin da kasar Sin ke ciki, da kaddamar da sha’anin zamanintar da kasar Sin mai tsarin mulkin gurguzu, kuma babban mutum da ya jagoranci Sinawa, wajen kyautata makomarsu da fuskar kasa, kana wanda ya taka rawa a sha’anin ‘yantar da al’umommin da ake musgunawa, da raya ci gaban bil Adama a duniya.

Xi Jinping ya kuma jaddada cewa, ci gaba da gudanar da sha’anin da marigayi Mao Zedong ya kaddamar, shi ne mataki mafi dacewa na tunawa da shi.

Ko da yake, Mao Zedong ya rasu yau shekaru 47 da suka gabata, amma al’ummar kasar Sin ba su manta da shi ba. Marigayi Mao Zedong ya canza tarihin Sin a zamanin kusa, har ma ya tabbatar da ci gaba da kuma farfadowar Sin, Sin ta samu tasowa daga matsayin maras karfi da koma baya zuwa mai karfi da wadata. (Amina Xu)