logo

HAUSA

Ya kamata kamfanonin Sin masu zaman kansu su sauke nauyinsu a zamantakewar al’umma

2023-12-27 14:26:30 CMG Hausa

Kungiyar hadin gwiwar masana’antu da ciniki ta kasar Sin, ta gabatar da rahoton alhakin dake wuyan kamfanonin Sin masu zaman kansu na shekarar 2023, inda aka yi nuni da cewa, a shekarar 2022, kamfanonin Sin masu zaman kansu sun bi sabon tunanin samun bunkasuwa, da shiga sabon tsarin samun bunkasuwa, da neman cimma burin samun wadata tare, da yin kokari a fannonin kiyaye samun bunkasuwa, da kara samar da aikin yi, da biyan haraji, da yin kirkire-kirkire, da farfado da kauyuka, da kiyaye muhalli, da ba da tallafi ga masu bukata da sauransu, wadanda suka samar da muhimmiyar gudummawa ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar.

A takaice, an kiyaye bunkasuwar kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin a shekarar 2022, wadanda suka kara sauke nauyinsu a zamantakewar al’umma. Na farko kamfanoni masu zaman kansu na kasar Sin sun sa kaimi ga ci gaban kasa. A shekarar 2022, yawan kudin da aka samu daga shige da fice na kamfanoni masu zaman kansu ya karu da kaso 12.9 cikin dari bisa na makamancin lokacin shekarar 2021, wanda ya kai kashi 50.9 cikin dari bisa adadin cinikin waje na kasar Sin. Na biyu, kamfanonin sun samar da guraben aikin yi da yawa. Na uku, sun samu nasarori daga yin kirkire-kirkire. Na hudu, kamfanonin sun shiga aikin farfado da yankunan karkara. Na biyar, sun zurfafa samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba. Na shida, sun shiga aikin sa kai cikin himma. (Zainab)