logo

HAUSA

Nana Akufo-Addo: Tattalin arzikin Ghana na farfadowa

2023-12-27 10:07:58 CMG HAUSA

 

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya ce tattalin arzikin kasarsa na farfadowa sannu a hankali cikin shekarun baya bayan nan, bayan kalubalen da ya fuskanta shekaru 3 da suka gabata.

Cikin sakonsa na taya murnar bikin Kirsimeti ga mabiya addinin Kirista dake kasar a ranar Litinin, shugaba Akufo-Addo ya ce Ghana na farfadowa daga wahalhalu da ta fuskanta da ma sauran sassan duniya a shekaru 3 da suka shude.

Ya ce, "Hauhawar farashi na raguwa, ana samun daidaito a bangaren darajar canjin kudade, kana tattalin arzikinmu na farfadowa. Kasarmu ba ta gama warwarewa ba, amma akwai kwarin gwiwar cewa, bisa aiki tukuru da dagewa za mu kai gaci, kuma za mu kai ga tsara makomarmu tare."

Daga nan sai shugaban na Ghana ya yi kira ga al’ummar kasar da su rungumi baki masu zuwa yawon bude ido a wannan lokaci na bukukuwa hannu biyu-biyu, ta yadda hakan zai baiwa kasar damar bunkasa harkokin zamantakewa da tattalin arziki da al’adu. (Saminu Alhassan)