logo

HAUSA

Jirgin ruwa mai binciken teku na farko na kasar Sin ya gwada yin aiki cikin nasara

2023-12-27 10:03:13 CMG Hausa

A yau ne jirgin ruwa irinsa na farko mai binciken teku da kasar Sin ta kera da kanta, wato jirgin ruwa samfurin “Dream” ya gama gwajin aiki na farko a yankin tekun bakin kogin Zhujiang na kasar Sin. Bisa sakamakon da aka samu daga gwajin, tsarin aikin jirgin ya dace da ma’aunin duniya.

Jirgin ruwan “Dream”, ya yi tafiya a teku har ta kimanin “Nautical miles” 500, kana ya samu nasarar gwajin muhimman ayyuka 19, da gama aikin hakar abubuwa a cikin teku bisa ka’idojin kasa da kasa masu nasaba. Ban da ayyukan gwajin tsarin jirgin ruwan, an kuma yi gwajin jirgin a fannin sabawa yanayin teku.

An ce, jirgin ruwan “Dream” mai binciken teku na kasar Sin, ba shi da nauyi sosai, kana yana iya aiwatar da ayyuka iri daban daban, yana iya tsayawa a yawancin tasoshin jiragen ruwan teku na kasa da kasa, kana yawan kudin da aka kashe wajen gina jirgin, da aiwatar da aikin jirgin ya ragu da kashi 40 cikin dari, idan aka kwatanta shi da sauran jirgin ruwan bincike na duniya. (Zainab)