logo

HAUSA

Sin ta yi nasarar harba tare da gwada taurarin dan adam na C karo na 24

2023-12-26 11:09:48 CMG Hausa

A yau ne, da misalin karfe 6 da mituna 39 na safe, cibiyar harba tauraron dan-Adam ta Taiyuan ta kasar Sin ta yi amfani da rokar Long March 11 ta yi nasarar harba taurarin dan adam na gwaji mai lamba 24C guda uku a tekun dake kusa da birnin Yangjiang na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin.

Taurarin sun kuma shiga sararin samaniya, kuma aikin harba su ya gudana cikin nasara kamar yadda aka tsara.

Ana amfani da taurarin samfurin 24C ne wajen gudanar da gwaje-gwajen kimiyyar sararin samaniya da kuma ayyukan fasaha.

Wannan shi ne karo na 503 da aka yi amfani da rokar Long March, wajen harba taurarin dan-Adam. (Ibrahim Yaya)