logo

HAUSA

Sin za ta dauki matakan da suka dace kan kamfani da wasu mutanen Amurka da suka shafi batun Xinjiang

2023-12-26 21:22:44 CMG Hausa

Dangane da sabon yunkurin da kasar Amurka ke yi na yada labaran karya da suka shafi jihar Xinjiang, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta sanar a taron manema labarai da aka saba yi a yau Talata ranar 26 ga wata cewa, kasar Sin za ta dauki matakan da suka dace daidai da doka kan wani kamfanin tattara bayanan sirri da wasu ma'aikata biyu na Amurka, wadanda suka samar da abin da ake kira tushen takunkumin da Amurka ta kakaba wa Xinjiang ba bisa ka'ida ba.

Da take amsa tambayoyin manema labarai, jami’ar ta bayyana cewa, Amurka ta sake kirkiro da yada labaran karya da suka shafi jihar Xinjiang, ta kuma yi amfani da abin da take kira batun kare hakkin bil'adama a jihar Xinjiang a matsayin uzuri na kakaba takunkumi ba bisa ka'ida ba kan jami'ai da kamfanoni na kasar Sin, ta hakan ta tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin sosai, da matukar keta dokokin kasa da kasa da ka'idojin da suka shafi huldar kasa da kasa, kana da bata sunan kasar Sin sosai, da lalata hakki da moriyar jami'ai da kamfanonin kasar Sin da abin ya shafa.

An kuma bayar da rahoton cewa, a ranar Jumma’ar da ta gabata bisa agogon wurin, shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya rattaba hannu kan "Dokar ba da izini kan tsaron kasa a kasafin kudi ta shekarar 2024", wadda ta kunshi munanan tanade-tanade da suka shafi kasar Sin. Game da wannan batu, jami’ar ta yi nuni da cewa, kudurin dokar ya yi katsalandan a harkokin cikin gidan kasar Sin, da karfafa goyon bayan Amurka ga Taiwan a fannin aikin soja, wadda ya saba wa manufar kasancewar Sin daya tak a duniya, da kuma sanarwoyin hadin gwiwa guda uku na Sin da Amurka.

Jami’ar ta kara da cewa, kasar Sin ta yi kira ga Amurka da ta cika alkawarin da shugaban kasar ya dauka na cewa ba za ta goyi bayan ‘yancin Taiwan ba, da daina yin amfani da batun Taiwan, tare da daina kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan. (Mai fassara: Bilkisu Xin)