logo

HAUSA

Kwamitin Kolin JKS ya gudanar da taron tunawa da cika shekaru 130 da haihuwar Mao Zedong

2023-12-26 20:09:44 CMG Hausa

A safiyar yau Talata ne kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS ya gudanar da taro a babban dakin taron jama’a domin tunawa da cika shekaru 130 da haihuwar marigayi kwamared Mao Zedong.

Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kasar Sin kuma shugaban kwamitin koli na soja, ya gabatar da muhimmin jawabi a wurin taron.

Shugaba Xi ya jaddada ciyar da manufar da marigayi kwamared Mao Zedong ya kafa gaba, ya kuma yi kira da a yi kokarin gina kasar Sin ta zama kasa mai karfi, da kuma farfado da ita daga dukkan bangarori ta hanyar zamanantarwa irin ta kasar Sin.

Manufar Mao Zedong wata dukiya ce mai kima ta ruhaniya ga jam'iyyarmu, kuma za ta jagoranci ayyukanmu na dogon lokaci, a cewar Xi, yana mai jaddada cewa, hanya mafi kyau na tunawa da marigayi Kwamared Mao Zedong ita ce ci gaba da ciyar da manufarsa gaba. (Yahaya)