logo

HAUSA

Firaministan Sin ya yi kira da a dunkule ci gaba da tsaron kasashen rukunin Lancang-Mekong

2023-12-26 10:35:47 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya yi kira ga kasashen dake rukunin Lancang-Mekong, da su dunkule harkokin ci gaba, da tsaron su wuri guda.

Li Qiang, wanda ya yi kiran a jiya Litinin, yayin taro na 4 na hadin gwiwar manyan jami’an kasashen rukunin ko LMC, wanda ya gudana ta kafar bidiyo, ya kuma bayyana alkawarin Sin na samar da rancen musamman, domin bunkasa ci gaban rukunin kasashen.

Firaminista Li Qiang, da shugaban Myanmar Min Aung Hlaing ne suka jagoranci taron, ya kuma samu halartar firaministocin Cambodia Hun Manet, da Laos Sonexay Siphandone, da Thailand Srettha Thavisin, da Vietnam Pham Minh Chinh.  (Saminu Alhassan)