logo

HAUSA

Adadin wadanda suka rasu sakamakon girgizar kasa a Qinghai ya karu zuwa 32

2023-12-25 10:36:38 CMG Hausa

Adadin mutanen da aka tabbatar da rasuwar su sakamakon girgizar kasa mai karfin maki 6.2, da ta auku a lardin Qinghai na arewa maso yammacin kasar Sin ya karu zuwa mutane 32.

A cewar mahukuntan yankin, girgizar kasar ta auku ne da tsakar daren ranar 18 ga watan nan, kuma bayan aukuwar ta an gudanar da ayyukan ceto da na tallafin jin kai, a yanzu kuma ana ci gaba da neman wasu mutane 2 da suka bace.  (Saminu Alhassan)