logo

HAUSA

Kasar Sin ta ware yuan miliyan 400 don taimakawa wadanda bala’in girgizar kasa ya shafa a Gansu da Qinghai

2023-12-25 19:32:17 CMG Hausa

Ma’aikatar kudi ta kasar Sin da ma’aikatar agajin gaggawa a yau Litinin sun kara ware wani kaso na tallafin agaji na yuan miliyan 400, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 56 a matsayin kudin agaji ga lardunan Gansu da Qinghai dake arewa maso yammacin kasar Sin, inda aka fi mai da hankali kan sake tsugunar da jama’a da samar da taimako ga iyalan wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasa mai karfin maki 6.2 da ta auku a makon da ya gabata. (Yahaya)