logo

HAUSA

Sin ta fitar da hasashen jimillar hatsin da ake fatan girbewa a 2024

2023-12-25 15:39:43 CMG HAUSA

 

Ma’aikatar noma da raya karkara ta kasar Sin, ta fitar da hasashen jimillar hatsin da kasar za ta girbe a shekarar 2024 mai zuwa, da nufin daidaita yawan abincin da ake sarrafa daga nau’o’in hatsi, da masara da waken soya, da fadada wuraren noma “rapeseed”, da bunkasa yabanyarsa.

Ma’aikatar ta ce Sin ta himmatu wajen wanzar da filayen noma da ake da su, tare da lalubo damammakin fafada su, da samar da karin yabanya daga gare su. Burin a cewar ma’aikatar shi ne samar da jimillar hatsi har sama da jin tiriliyan 1.3, kwatankwacin kilogiram biliyan 650 a shekarar ta 2024.  (Saminu Alhassan)