logo

HAUSA

Sin ta harba taurarin dan Adam 4 na binciken yanayi

2023-12-25 11:25:44 CMG HAUSA

 

Da karfe 9 na safiyar Litinin din nan ne kasar Sin ta yi nasarar harba wasu taurarin dan Adam guda 4, na binciken yanayi zuwa samaniya, daga cibiyar harba kumbuna ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar.

Taurarin dan Adam din, na cikin rukunin Tianmu-1 na binciken yanayi, an kuma harba su ne ta amfani da rokar Kuaizhou-1A, kuma sun shiga falakin su cikin nasara.

Muhimmin aikin su shi ne samar da nau’o’in bayanai, don hidimomin hasashen yanayi na kasuwanci. (Saminu Alhassan)