logo

HAUSA

Xi ya gabatar da umarnin karin girma ga hafsoshin soji zuwa mukamin Janar

2023-12-25 20:57:19 CMG Hausa

Shugaban hukumar koli ta soji (CMC) ta kasar Sin Xi Jinping a ranar Litinin din nan ya gabatar da takardar shaidar tabbatar da karin girma ga hafsoshin soja biyu zuwa mukamin Janar.

Hafsoshin da aka kara wa girman dai sun hada da kwamandan siyasa na dakarun kudanci na rundunar sojin ‘yantar da jama’a ta kasar Sin(PLA) Wang Wenquan, da kwamandan sojojin ruwa na PLA Hu Zhongming.

Mukamin Janar shi ne matsayi mafi girma ga hafsoshi a cikin hidimar aikin soja a kasar Sin. (Yahaya)