logo

HAUSA

An wallafa littafin Xi Jinping game da BRI bugun shekarar 2023

2023-12-25 10:21:53 CMG Hausa

Kamfanin dab’i na JKS, ya wallafa littafin shugaban kasar Sin Xi Jinping, game da shawarar ziri daya da hanya daya ko BRI bugun shekara ta 2023.

Littafin ya kunshi muhimman bayanai ko rubuce rubuce 78 masu nasaba da BRI, wadanda shugaba Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS ya gabatar, tsakanin watan Satumban shekarar 2013 zuwa Nuwamban 2023.

Shawarar BRI, wadda shugaba Xi ya gabatar, ta mayar da hankali ne ga raya burikan bai daya na al’ummun kasashe daban daban, domin samar da zaman lafiya da ci gaba, tare da samarwa duniya tsarin walwala da ci gaban bai daya.  (Saminu Alhassan)