logo

HAUSA

Zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar Sin ya fara zamansa

2023-12-25 10:48:44 CMG Hausa

Zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 14, ya fara zama na bakwai a yau Litinin, don duba daftarin dokoki da yiwa wasu dokoki da dama gyare-gyare.

Ajandar zaman ta hada da sake bitar wani daftarin dokar majalisar gudanarwa ta kasa, da daftarin dokar dake shafar kamfanoni da aka yiwa gyaran fuska, da gyaran daftarin dokar bayar da tallafi, da daftarin dokar samar da abinci, da gyaran daftarin dokar aikata manyan laifuka, da daftarin dokar mayar da martani, da daftarin doka kan gama garin kungiyoyin raya tattalin arzikin yankunan karkara.

'Yan majalisar za su kuma duba daftarin yin gyare-gyare ga dokar sanya ido ta zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'a a dukkan matakai, da daftarin yin kwaskwarima ga dokar kiwon lafiya da killacewa, da daftarin yin kwaskwarima ga dokar albarkatun ma'adinai da sauransu. (Ibrahim)