logo

HAUSA

Ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil’adam ya haifar da gagarumin ci gaba a harkokin duniya

2023-12-25 20:28:14 CMG Hausa

Shekarar da muke ciki shekara ce ta cika shekaru 10 da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da ra’ayin gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adam. Da take amsa tambayoyin da suka shafi batun a yau Litinin ranar 25 ga wata, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Mao Ning ta ce, an shigar da ra’ayi din cikin kudurorin babban taron MDD na tsawon shekaru bakwai a jere, kuma sau da yawa aka rubuta shi cikin kudurori ko sanarwoyi na tsare-tsare na bangarori da dama, ciki har da kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, da BRICS da dai sauransu, wanda ya haifar da muhimmin ci gaba a harkokin mulkin duniya a fannoni da dama.

Jami’ar ta kara da cewa, kasarta a shirye take ta yi aiki tare da kasashen duniya wajen gina budaddiyar duniya mai tsafta da kyau dake samun dauwamammen zaman lafiya, tsaro da wadata tare, ta yadda za a samar da makoma mai kyau ga bil’adama.

Yayin da take bayyana matsayinta kan bikin bazara da aka kebe a matsayin ranar hutu na MDD, jami’ar ta yi nuni da cewa, bikin bazara na kasar Sin ne da duniya baki daya. Muna son mu yi bikin bazara tare da sauran kasashen duniya, kuma muna fatan cewa al'ummomi daban daban za su iya kasancewa tare cikin jituwa, cimma nasara tare da koyi da juna. Muna kuma fatan jama'ar kasashe daban daban za su kara fahimtar juna, kuma su yi aiki kafada da kafada da juna don gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil'adama. (Mai fassara: Bilkisu Xin)