logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya ziyarci yankunan da suka yi fama da bala’in girgizar kasa

2023-12-24 16:54:49 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ziyarci yankunan da suka sha fama da girgizar kasa a arewa maso yammacin kasar Sin a jiya Asabar, inda ya yi kira da a dauki dukkanin matakan da suka kamata, wajen kyautata yanayin rayuwar mazauna wuraren.

Li, ya ziyarci kauyuka da dama a gundumar Jishishan dake lardin Gansu, da gundumar Minhe dake lardin Qinghai mai makwaftaka.

Yayin ziyarar ta sa ya zanta kai tsaye da mutanen da ibtila’in ya shafa, ya kuma ji yadda ayyukan samar musu matsugunai, da tallafin jin kai, da sake gina wuraren zaman su ke gudana. Kaza lika, ya ce muhimmin abun da ake so a cimma nasarar sa cikin ayyukan jin kai shi ne tabbatar da jama’ar da bala’in ya shafa sun samu muhalli mai kyau mai dumi a wannan lokaci na hunturu.

Firaministan na Sin ya kara jaddada kira ga ma’aikatan jin kai da su kara azamar samar da kayayyakin bukata, da na amfanin yau da kullum ga mazauna wadannan yankuna, tare da gina gidajen wucin gadi cikin sauri ga wadanda ke zaune a tantuna.

Ya kuma ba da umarnin sake duba gine gine, da karfafa wadanda suka kamata, ta yadda mutane za su iya komawa, tare da samun damar sake bude muhimman ababen more rayuwa kamar makarantu da asibitoci.

Da misalin karfe 12 saura minti 1 na daren ranar Litinin din makon jiya ne girgizar kasar mai karfin maki 6.2 ta auku. Kuma ya zuwa ranar Juma’a, adadin wadanda ta hallaka ya kai mutane 148, baya ga mutane 781 da suka jikkata. Kana ibtila’in ya lalata gine gine da dama. (Saminu Alhassan)