logo

HAUSA

Wadanda suka jikkata yayin girgizar kasa a kasar Sin sun samu kulawar da ta dace

2023-12-24 17:25:12 CMG Hausa

A yau Lahadi 24 ga watan nan ne hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin, ta gudanar da taron manema labarai. Inda yayin taron, kakakin hukumar Mi Feng ya bayyana cewa, kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta Sin, da majalissar gudanarwar kasar, a ko da yaushe suna damuwa da halin da jama'ar yankunan Gansu da Qinghai da girgizar kasa ta shafa ke ciki.

Mi Feng ya ce ya zuwa yanzu, dukkanin wadanda suka jikkata a wannan girgizar kasar sun samu kulawar da ta dace a kan lokaci, an kuma maido da ayyukan bincike, da jiyya na yau da kullum a yankunan da bala'in ya afku.

A cewar jami’in, hukumar lafiya ta kasar Sin, za ta yi aiki tare da hukumar kula da magungunan gargajiya ta kasar Sin, da hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasar, wajen kara hada kan kayayyakin aikin jinya, da karfafa ma'aikatan jinya a yankunan da bala'i ya rutsa da su, kana suna yin iyakacin kokarinsu wajen jinyar wadanda suka jikkata, da ci gaba da gudanar da sa ido, da tantance hadarin cututtuka masu yaduwa, da kuma gudanar da aikin sa ido kan ruwan sha, da kashe kwayoyin cuta, da sauran ayyukan kiyaye lafiya da na shawo kan annoba, don tabbatar da dakile aukuwar wata babbar annoba bayan bala'in. (Mai fassara: Bilkisu Xin)