logo

HAUSA

An fara gina cibiyar UHD Highland ta CMG

2023-12-23 19:38:22 CMG Hausa

A yau Asabar 23 ga wannan watan ne aka fara gina cibiyar kirkire-kirkire ta UHD ta CMG, ko CMG UHD Highland a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Yayin bikin kaddamar da aikin, shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi, inda ya bayyana cewa, gina cibiyar ta UHD, muhimmin mataki ne da CMG ya dauka, domin kara karfafa cudanyar dake tsakanin kafofin watsa labarai na birnin Beijing. Kuma nan gaba sassan biyu, wato CMG da gwamnatin birnin Beijing za su gudanar da hadin gwiwa, ta yadda za su kafa cibiyar UHD da matsayinta zai kai sahun gaba a fadin duniya, kuma da hakan masu kallo za su kara jin dadin kallon hotunan bidiyo mafiya inganci da za a samar ta fasahohin zamani. (Jamila)