logo

HAUSA

Sin na fatan Amurka za ta ci gaba da aiwatar da matakan hadin gwiwa na yaki da bazuwar miyagun kwayoyi tare da Sin bisa martaba juna

2023-12-22 19:35:09 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce ci gaban da aka samu karkashin hadin gwiwar Sin da Amurka ta fuskar yaki da bazuwar miyagun kwayoyi bai zo da sauki ba, don haka ya dace sassan biyu su martaba sakamakon yadda ya kamata.

Wang, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na Juma’ar nan, ya yi fatan cewa bangaren Amurka zai kwatanta gaskiya, ya yi kokarin daidaitawa da Sin, kana ya ci gaba da aiwatar da matakan hadin gwiwa na zahiri, a fannin na yaki da bazuwar miyagun kwayoyi bisa mutunta juna, da daidaito, da cimma moriya tare.

Wang ya yi bitar nasarar baya bayan nan da sassan biyu suka cimma, a fannin yaki da bazuwar miyagun kwayoyi, bayan taron shugabannin kasashen a birnin San Francisco, yana mai cewa, hadin gwiwar sassan biyu a fannin, na daya daga cikin muhimman matakai da shugabannin biyu suka amincewa a ganawar San Francisco.

Daga nan sai ya ce domin aiwatar da wannan muhimmin mataki, Amurka ta janye takunkuman da ta kakabawa hukumomin tsaron Sin masu nasaba da aikin. Ya ce a baya bayan nan, Sin ta ci gaba da yayata muhimman matakai, na yaki da kwayar fentanyl, da sauran sanadaran hada ta.   (Saminu Alhassan)