logo

HAUSA

Rahoto: Sin Ta Kasance A Kan Gaba A Fannin Tattalin Arziki Na Zamani A Asiya

2023-12-22 09:47:31 CMG Hausa

Wani rahoton tattalin arziki na zamani na yankin Asiya na shekarar 2023 da aka fitar jiya Alhamis ya nuna cewa, kasar Sin tana kan gaba a fannin tattalin arziki na zamani, inda darajarsa ta kai dalar Amurka tiriliyan 7.47 a shekarar 2022.

A cewar wannan rahoto da aka fitar, yayin wani taron da babban sakataren dandalin Boao na Asiya Li Baodong ya gabatar a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, kasar Japan ce ta biyu da darajar da ta kai dalar Amurka tiriliyan 2.37, sai kasar Koriya ta Kudu mai darajar dalar Amurka biliyan 952.3.

Li ya ce, kasar Sin tana daya daga cikin kasashen duniya, da tattalin arzikin zamaninsu ya fi samun kyakkyawan yanayin ci gaba mai inganci, da saurin bunkasuwa, da ma yadda ake cin gajiyarsa.

A cewarsa, babban taron kolin ayyukan raya tattalin arziki na kasar Sin da aka gudanar a baya-bayan nan, ya jaddada kokarin da ake na inganta sabbin masana'antu, da bunkasa tattalin arzikin zamani. Yana mai cewa, ana sa ran wannan rukuni na tattalin arziki, zai ci gaba da zama muhimmin karfi ga ci gaban tattalin arzikin kasar Sin.(Ibrahim)