logo

HAUSA

Sin na maraba da Amurka a fannin musaya da hadin gwiwar ayyukan binciken samaniya

2023-12-22 19:46:32 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce har kullum Sin na maraba da Amurka, a fannin musaya da hadin gwiwar ayyukan da suka shafi binciken sararin samaniya. Wang, ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na Juma’ar nan.

Wasu rahotannin baya bayan nan sun hakaito jakadan Amurka a kasar Sin Robert Nicholas Burns, na cewa wai Sin ba ta da niyyar yin hadin gwiwa da Amurka a fannin binciken duniyar wata, kuma fannin zai kasance wani fage guda ga kasashen biyu.

Game da hakan, Wang Wenbin ya ce gwamnatin kasar Sin ta sha bayyana aniyarta ta bunkasa bincike, da amfani da sararin samaniya ta hanyoyin zaman lafiya, kuma a shirye take ta gudanar da musaya, da hadin gwiwa tare da sauran kasashen duniya bisa daidaito, da cimma moriya tare, da kuma bunkasa fannin tare da juna, da ingiza gina al’umma mai makomar bai daya a fannin binciken sararin samaniya.

Wang Wenbin ya jaddada cewa, idan har da gaske ne Amurka na son ingiza musaya, da hadin gwiwa tare da Sin a wannan fanni, to kamata ya yi ta kawar da dokokin ta dake yin tarnaki ga hakan, ta kuma dakatar da bayyana kalamai marasa dacewa, kana ta aiwatar da matakai na zahiri, na kawar da duk wani shinge dake dakile hadin gwiwar sassan biyu. (Saminu Alhassan)