logo

HAUSA

’Yan sama jannati na kumbon Shenzhou-17 sun gama aiki a wajen kumbo a karon farko

2023-12-22 10:14:08 CMG Hausa

Jiya Alhamis, ’yan sama jannatin kumbon Shenzhou-17 sun yi nasarar gudanar da aiki a wajen kumbo a karo na farko, inda suka kammala ayyukan da aka tsara yadda ya kamata, kamar gyara farantan dake tattara makamashin hasken rana na kumbon Tianhe da sauransu. Dan sama jannatin kasar Sin Yang Hongbo, ya dawo aiki a tashar sararin samaniyar kasar Sin, bayan shekaru biyu da ya yi aiki a tashar a karo na farko, kuma shi ne dan sama jannati da ya yi aiki sau biyu a tashar.

Haka kuma, dan sama jannati Tang Shengjie wanda aka haife shi a watan Disamba na shekarar 1989, shi ne dan sama jannati mafi karancin shekaru cikin ’yan sama jannatin kasar Sin da suka taba aiki a wajen kumbon.

Bisa shirin da aka tsara, za a gudanar da ayyukan da suka shafi gwaje-gwajen kimiyya da fasaha da wasu gwaje-gwaje masu dimbin yawa a wa’adin aikin kumbon Shenzhou-17, ana sa ran ’yan sama jannati za su gudanar da ayyuka da dama a wajen kumbo. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)