logo

HAUSA

Taron shugabannin JKS ya yi kira da a kara dogaro kan ginshikai masu kwari wajen kara farfado da kasa

2023-12-22 19:57:44 CMG Hausa

Taron shugabannin JKS, ya jaddada bukatar dorawa kan nasarorin da aka cimma bisa shirin nazarin akidun JKS, ta yadda za a kai ga iya dogaro ga ginshikai masu kwari, na gina kasa mai karfi, da ingiza farfadowar kasa.

Babban sakataren kwamitin kolin JKS, kuma shugaban kasar Xi Jinping, shi ne ya jagoranci taron da ya gudana daga jiya Alhamis zuwa yau Jumma’a, inda ya gabatar da muhimmin jawabi.

Taron ya maida hankali ne ga nazarin sassan da ya dace a inganta, da nazarin wuraren gazawa, ya kuma gudana ne karkashin ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. (Saminu Alhassan)