logo

HAUSA

Jarin waje na kai tsaye dake shigowa Sin ya kai yuan tiriliyan 1.04 cikin watanni 11 na farkon bana

2023-12-21 20:23:07 CMG Hausa

Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce jarin waje na kai tsaye dake shigowa Sin wato FDI , ya kai yuan tiriliyan 1.04 cikin watanni 11 na farkon shekarar bana.

Alkaluman ma’aikatar ya nuna cewa, jarin na FDI da ake amfani da shi a babban yankin kasar ya kai yuan tiriliyan 1.04, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 146.45 cikin watannin 11, wanda ya yi kasa da na shekarar da ta gabata da kaso 10 bisa dari.

Tsakanin watannin 11, sabbin kamfanoni masu zuba jarin kai tsaye  48,078 ne suka bude hada hada a kasar ta Sin, adadin da ya karu da kaso 36.2 bisa dari a shekara.

Har ila yau, a cewar ma’aikatar, alkaluman FDI a fannin kamfanonin manyan fasahohi ya daga da kaso 1.8 bisa dari a shekara, yayin da na fannin samar da kayayyakin bukata a fannin kiwon lafiya ya daga da kaso 27.6 bisa dari, sai kuma na fannin sadarwa da ya karu da kaso 5.5 bisa dari.

Kaza lika, a tsakanin wannan wa’adi, FDI daga kasashen Birtaniya ya kasu da kaso 93.9, daga Faransa ya karu da kaso 93.2, sai na Netherlands da ya karu da kaso 34.1 bisa dari.  (Saminu Alhassan)