logo

HAUSA

Manufar Sin ta hadin kan wanzar da zaman lafiya da daidaito a tekun kudanci tare da mambobin ASEAN ba ta sauya ba

2023-12-21 19:40:33 CMG Hausa

Yayin taron manema labarai na Alhamis din nan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya jaddada matsayar kasar Sin game da matakan shawo kan sabani, ta hanyar tattaunawa da gudanar da shawarwari, matsayar da jami’in ya ce har yanzu ba ta sauya ba.

Kaza lika, aniyar Sin ta aiki tare da kasar Philippines, don aiwatar da yarjejeniya, da matakan fahimtar juna tsakanin su, hakan ma bai sauya ba. A daya bangaren kuma, manufar Sin game da hada kai don wanzar da zaman lafiya da daidaito a yankin tekun kudanci, tare da kasashe mambobin kungiyar ASEAN, ciki har da Philippines, ita ma ba ta sauya ba.

Wang, wanda ke tsokaci game da takaddamar Sin da Philippines don gane da batun teku, ya ce tabbas Sin za ta tsaya tsayin daka wajen kare ikon mulkin kai, da halastattun hakkoki da moriyar ta, wanda hakan ba zai taba sauyawa ba.

Daga nan sai ya yi fatan cewa, Philippines za ta yi zabi na gari, ta aiwatar da sahihan matakai na zama lafiya tare da makwaftanta, ta kuma yi aiki tare da Sin, don warware batun teku dake tsakanin ta da Sin. (Saminu Alhassan)